Dan wasa Gareth Bale ya ci wa Real Madrid kwallo ta uku, wadda kuma ita ce kwallo ta 100 da ci wa Madrid tun daga fara wasan sa a kungiyar.
Wannan wasa ya matsa da Real Madrid zuwa matsayin ta biyu kenan kasa da Barcelona.
Casemiro na Madrid ne ya fara jefa kwallo a ragar Atletico, tun a minti na 16 da fara wasa, yayin da Greizman ya rama a minti na 24.
Sai dai kuma Real ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, wanda kaftin din su, Sergio Ramos ya buga kuma ya yi nasara a minti na 42.
A minti na 74 kuma Gareth Bale ya kara jefa kwallo ta 3 a ragar Atletico. Sai dai kum a minti na 80 an ba Thomas na Atletico jan kati, inda aka tashi wasan 1-3.
HUCE HAUSHI: Magoya bayan Atletico sun ragargaza mutum-mutumin Cortious na Real Madrid.
Tun kafin a fara wasa wasu magoya bayan kungiyar Atletico suka ragargaza mutum-mutumin tsohon dan wasan su, kuma mai tsaron gidan Real Madrid a yanzu, Cortious Thibous.
Mai tsaron gidan wanda Chelsea ta saya tun a cikin 2010 ya na matsahim sai ta bada aron sa ga Atletico cikin 2011 domin ya kara gogewa a La Liga, bayan David de Gea na Atletico ya koma Manchester United a Ingila.
An ji dadi shekaru uku da ya shafe a kungiyar inda ya haifar musu da samun nasarorin lashe kofuna da dama. Ya buga wasanni 150, inda a cikin 2014 ya koma kungiyar sa ta asali, wato Chelsea da ke Landan.
Daga Chelsea ne a karshen kakar 2017/2018 Real Madrid ta saye shi. wannan abu bai yi wa mayoya bayan Atletico dadi ba, ganin yadda tsohon mai tsaron gidan su ya koma kungiyar da suka fi adawa da ita a duk duniya, kuma wadda su ke gari daya.
A yau kafin a fara wasa, wasu mafusata suka je wajen filin kwallon inda aka yi mutum-mutumin mai tsaron gidan a lokacin da ya ke kungiyar suka ragargaza shi, tare da jibga masa beraye na roba da kuma tulin kwalaben giyar da aka shanye ruwan giyar da ke ciki.
Discussion about this post