Rashin fitowar jama’a ne yasa ban iya cika alkawarin sama wa Buhari kuri’u miliyan 5 ba a Kano – Inji Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa rashin fitowar jama’a ne ya sa bai iya cika alkawarin da yayi ba na sai ya tabbata Buhari ya samu kuri’u miliyan 5 ba a Kano.

Ya kuma ce duk wadanda suke da ja bisa yawan kuri’un da Buhari ya samu suna da karancin hanlkali sannan basu kaunar tsarin mulkin dimokradiyya.

Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Kano ya nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi da kuri’u 1,464,768 shi kuma Atiku Abubakar ya samu kuri’u 391,593.

Ko da yake an sami matsaloli a wasu rumfunar zabe dake kananan hukumomi 17 a jihar inda ya sa aka soke zaben da aka yi a wuraren, an yi zabe cikin kwanciyar hankali kuma bisa tsarin dokar zabe.

Ganduje ya kuma ce abin da ya faru a zaben ranar Asabar nuni ne na yadda jam’iyyar su za ta yi nasara a zaben gwamna mai zuwa.

” A zaben nan da aka kammala jam’iyyar APC ta yi nasara a shugaban kasa, sannan ta lashe duk kujerun sanatoci uku dake jihar da kujeru 26 na majalisar Tarayya.

” Haka na tabbatar mana da cewa za mu kara samun nasara a zaben da zai gudana ranar 9 ga watan Maris.”

Share.

game da Author