Tun karfe 11 na rana dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya dira filin jirgin sama na Malam Aminu Kano. Amma saboda cinkoson jama’a sai da ya shafe awa hudu kafin ya isa Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Duk hanyar da ka duba jama’a ta ko’ina ke ta kwarara. Daga wadanda suka yi wa filin jirgi tsinke tun da safe, sai wadanda suka cika filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata tun da safiya.
Tun kafin karfe 12 na rana filin ya cika ya batse, ba masaka tsinke. Ba ka ganin komai idan ka kalli kan jama’a, sai jar hula, tambari da alamar cikamakin kamalar akidar kwankwasiya kenan.
A manya da ka na nan titinan Kano, musamman hanyoyin da suka nufi filin taro, ba komai sai tururuwar jama’a.
An yi taruka kamar biyar a tarihin Kano cikin shekarun baya na da na yanzu.
Na farko akwai taron bikin auren ‘ya’yan Sarkin Kano Abdullahi Bayero, wanda aka ce an yi gagarimin taro. Akwai kuma bikin attajiri marigayi Ado Dandawaki a lokacin da ya auri ‘yar Madakin Kano na lokacin, Bello Dandago, kafin shigowar shekarar 1980. Shi ma an ce Kano ta dinke.
Sai bikin fitacciyar ‘yar fim Fati Mohammed, wanda aka yi cikin 2001. Shi ma Kano ta ga ruwan jama’a, domin har matan aure masu ra’ayin finafinai da kaunar ‘yan fim, sai da wasun su suka dira Kano wurin shagalin bikin.
Taron kaddamar da Shari’ar Musulunci a 2000 a Kano ma ya kwashi gangamin dandazon jama’a.
Na baya-bayan nan shi ne wanda Buhari ya je kamfen a Kano, cikin 2015.
Na baya-bayan nan, shi ne wanda Buhari ya je kamfen a Kano kafin zaben 2015. Sai dai kuma duk wanda za ka tambaya zai ce maka bai taba ganin taron siyasa irin na zuwan Atiku Abubakar a Kano ba, har a lokacin marigayi Malam Aminu.
YADDA ATIKU YA SHIGA KANO
Bayan fitar sa daga jirgin sama, sun shiga cikin doguwar motar nan samfurin ‘civilian’. Cincirindon jama’a ya sa sun kasa bi ta Titin da ya doshi Akija Hotel zuwa gidan Jaridar Triumph, sai dai suka sake tsayawa ta cikin Kofar Ruwa, suka kutsa cikin Gwammaja, cibiyar da dan takarar sanata na Kano ta Tsakiya, na PDP, Hon. Ali Madaki ya ke.
Tun da motar da ke dauke da su Atiku ta fito daga filin jirgi, manyan da ke cikin motar sun rika watsa wa jama’a tutocin PDP.
Sai da suka shafe sa’o’i hudu kafin su isa kofar fadar Sarkin Kano. A cikin fadar, sai da Atiku ya shafe sama da awa 1:30 bai fito ba.
Dama tun safe an ajiye motar da aka tsara cewa ita ce za ta kwashe su daga gidan Sarki zuwa filin taro. Motar samfurin ‘Marco Polo’ budaddiya daga sama, ita ce ta dauki su Atiku, Bukola Saraki, Kwankwaso da sauran gaggan PDP zuwa filin taro.
A kan hanyar zuwa filin taro daga gidan sarki ma sun rika kwasar tutoci su na jefa wa jama’a.
“A BA MU A HUTA”
Ba ka jin komai daga bakin matasa sai kalmar “a ba mu a huta”, wadanda tafiye kawai su ke takasa, kamar dakarun da su ka ci gari da yaki.
Manya da dattawa da ke gefen titi su na kallon dubun-dubatar jama’a kuwa, wasu sai dai kabbara kawai su ke yi, saboda mamakin dandanzon jama’a. Dama kuma a jajibirin taro Kwankwaso ya shiga radiyo ya yi jawabin tsima magoya bayan sa, tare da cewa bai dauke wa kowa zuwa tarbar Atiku Abubakar ba.
‘YAN A-YI-TA-TA-KARE
Matasan ‘yan zafin kai da masu neman huce-haushin cin zarafin magoya bayan Kwankwaso da ‘yan APC suka rika yi, a karkashin shugabancin Abdullahi Abbas, Shugaban APC na Jihar Kano, a yau sun yi ramuwar gayya.
Tun daga Kofar Nassarawa har zuwa Gwale, unguwar su Abbas shugaban APC, sai da matasan Kwankwasiyya suka bi duk wata fasta mai dauke da hoton Buhari ko Ganduje, ko Abbas, kai ko ma wani dan APC, sun kekketa ta, ko sun ragargaza ta. Su dai ” a mu a huta” kawai.
JAJIBIRIN TARON KANO
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya shiga Radiyon Dala FM, ya ja kunnen malaman addini da su guji tsoma bakin su a cikin siyasa. Kwankwaso ya yi masu kakkausan gargadin cewa ya na sane cewa da yawan su tsuliyar su da kashi, kuma idan ta kama zai fallasa su daya bayan daya.
Ya ce idan mutum zai yi amfani da larabci ya ci musu mutunci don su na PDP, to su ma za su hau mimbarin siyasa su ci wa malamin mutunci.
A bangaren ‘yan siyasa kuwa, Kwankwaso a wani bidiyo ya ce daidai su ke da kowane mai mutunci daga sama har kasa. Kuma daidai su ke da “duk wani tantagaryar dan iska.”
Ya ce tun daga Shugaban Kasa har kan gwamna, ba wanda bai tsaya a kan mimbarin siyasa sun sa masa jar hula ba.
FICEWAR GANDUJE DAGA KANO
Ganduje da magoya bayan sa ba su yini a Kano ba, domin a yau Lahadi ya tafi taron jami’an dogarawan kula da zirga-zirgar ababen hawa, wato KAROTA, wanda ya gudanar a Karamar Hukumar Karaye.
TAWAGAR KAURAYE DA ‘YAN TAURI
Wanda bai taba ganin tantagaryar ‘yan tauri ba, to a yau ya yi kallo a Kano, amma fa sai mai jan halin da ya isa ya kusance su. An rika daga zandaren takobi sama, sannan a saddo tsinin takobin kasa ya rika digar ruwa har karfen takobin ya zama ruwa gaba daya ya na tsiyaye.
Wasu sun rika yi wa wukake taunar kuli-kuli, ko alewa ko rake.
