PDP ta yi wa APC zarra a Gwarimpa, Nyanya, Jikwoyi da sauran sassan Abuja

0

Yayin da aka kammala zabe da yammacin Asabar a fadin kasar nan, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba a yawancin unguwannin Abuja da kewaye a sakamakon da ya fara fitowa.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa ‘yan takarar jam’iyyar PDP ne ke kan gaba a zabukan shugaban kasa, majalisar dattawa da majalisar tarayya.

A mazabar FHA a Nyanya, PDP ta samu 84, ita kuma APC 28. A Makarantar Firamare Ta Nyanya kuma APC ta samu 67, ita kuma PDP 416. Wannan sakamakon zaben sanata ne.

A zaben shugaban kasa ma PDP ke da rinjaye da kuri’u 438, ita kuma APC kuri’u 67.

A rumfar zaben Orozo Primary School kuwa, PDP ta samu kuri’u 1375, ita kuma APC ta samu 308 a zaben shugaban kasa.

Haka sakamako da da makarantar Kugbo ya nuna, PDP na da 158, APC na da 129.

A rumfar 009A a Kugbo, PDP ta samu 483, ita kuma APC 84.

Haka ma a Jikwoyi, Galadima da City Gate, duk PDP ce a kan gaba.

A LEA Primary School, PDP ta samu 707 a zaben shugaban kasa, ita kuma APC 194.

Can a Gwarimpa Model School kuwa, PDP ta shige gaba can din ma da kuri’u 676, yayin da PDP ke da 272.

A Gwarimpa Model Gate, PDP ta samu kuri’u a dukkan zabukan uku sama da APC.

A Efab Life Camp kuma PDP ta lashe 883, ita kuma APC 258 duk a zaben shugaban kasa.

Wani abin lura da wannan sakamako shi ne, dukkan inda PDP ta yi rinjaye a zaben shugaban kasa. A nan majalisar dattawa da ta tarayya ma duk ita ce keyi.

Share.

game da Author