PDP ta yi kira ga hukumar zabe da ta hana Buhari takara a zaben 16 ga wata

0

Jam’iyyar PDP ta yi kira ga Hukumar Zabe mai Zaman Kanta da ta hana Buhari takara a zabe mai zuwa.

Shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus ne ya bayyana haka a wajen taron gangamin jam’iyyar a garin Enugu ranar Juma’a.

” Kowa ya gani kiri-kiri cewa an gayyato wasu gwamnonin kasar Nijar da suka halarci taron jam’iyyar APC domin yin amfani dasu wajen shirya magudi da aringizon kuri’u da karfin tsiya sannan kuma sun yi dakon makamai da kudade aboye zuwa kasar nan.

” A dalilin haka ina kira ga shugaban Hukumar Zabe na Kasa, Mahmood Yakubu da ya hana Buhari ci gaba da nuna kan sa a matasyin dan takara domin ya gayyato mana bakin haure su shigo su jagwalgwala mana zabe.

Issah Mousa na Zider da Zakiri Umar na Maradi ne suma halarci taron Buhari a Kano ranar Alhamis.

Ko da suka iso garin Kano sai suka ko saje da sauran ‘yan APC inda suma suka saka manyan kayan da akayi wa ado da tutar APC.

Jam’iyyar ta koka cewa abinda jam’iyyar APC ta yi ba daidai yake da yadda shirin Najeriya ya ke ba. Gayyato baki haka dauke da makamai sa makudan kudade domin mara wa wani baya a zabe ba saje da dokar Najeriya.

A dalilin haka ko jam’iyyar tayi kira da kakkausar murya da yin tir da wannan ziyara da wadannan gwamnonin Kasar Nijar suka yi.

Share.

game da Author