Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya yi tir da dage zaben da Hukumar INEC ta yi wanda ta kara sati daya kafin a gudanar da zabe.
A cikin wata sanarwa da kakakin yada labaran sa, Ike Abonyi ya fitar da jijjifin asubahin yau Asabar, Secondus ya ce kara wa’adin ranakun zaben wani gagarimin tuggu ne da Shugaba Muhammadu Buhari ya kulla da nufin kankamewa a kan kujerar mulki, duk kuwa da cewa ‘yan Najeriya sun gaji da shi, sun a so ya su sauke shi.
Shugaban INEC ne ya yi sanarwar kara wa’adin sati daya kafin a gudanar da zabe.
“Biyo bayan bin diddigi na yin nazarin tsare-tsaren da INEC ta yi da kuma irin yanayin yadda shirin na ta ke tafiya har zuwa yanzu, da kuma dalilan alkawarin da INEC din ta dauka cewa za ta gudanar da sahihin zabe kuma karbabbe, wannan hukuma ta cimma matsaya cewa gudanar da zabe a ranar Asabar ba zai yiwu ba.
“Dalilin haka INEC ta dage zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dattawa zuwa ranar 23 Ga Fabrairu, shi kuma na Gwamna da na Majalisar Jiha da na Kananan Hukumomin FCT zuwa ranar 9 Ga Maris, 2019.”
Secondus ya kara da cewa PDP ba za ta taba amincewa da sakamakon zaben da ba a yi shi cikin gaskiya, adalci, kwanciyar hankali, zaman lafiya ba.
Ya ce ba za ta taba amincewa da magudi, tuggu, cin zarafin ‘yan adawa, yi musu barazana a wurin jefa kuri’a ko waskiya ba.
“Saboda sun ga cewa sun kasa cimma burin su na tuggun da suka kitsa don ci gaba da zama kan mulki, sai APC da INEC suka kulla kutunguilar dage zabe. Wannan kuwa babbar barazana ce ga dimokradiyyar kasar nan. Ba za mu amince ba.” Inji Secondus.
Secondus ya kara yin zargin cewa APC da INEC sun rika hada kai wajen kokarin yi wa zabe makarkashiya, ciki har da kona ofisoshin zabe a wasu jihohi inda kayann zabe suka kone kurmus, don kawai su kirkiro matsalolin da babu su.
Ya kuma buga misali da kisan mutane 66 da aka yi a jajibirin zabe a Kaduna, cewa shiri ne da APC ta yi domin kawai ta firgita jama’a har su ji tsoron fita su jefa kuri’a.