PDP ta lashe rumfar zaben Osinbajo

0

Jam’iyyar PDP ta yi zarra a rumfar zaben Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, a Lagos.

Ta lashe dukkan mukaman ‘yan takara uku, na shugaban kasa, majalisar dattawa da ta tarayya.

PDP ta yi galaba ce a wurare biyu, inda ta lashe kuri’u 425, ita kuma APC ta samu 229 a zaben shugaban kasa.

A zaben sanata kuwa, PDP ta samu 414 ita kuma APC 261.

Zai kuma zaben dan majalisar tarayya, inda PDP ta samu 268, ita kuma APC 190.

Fitaccen mawakin nan Olubankole Wellington da aka fi sani da Banky W, ya samu kuri’u masu yawa fiye da dan takarar majalisar tarayya na APC a wannan rumfar zabe, domin ya samu har kuri’u 212.

An fara zabe ne 10:30, kuma an rufe 7 na yamma daidai. An kammala kirga kuri’u 12:20 na dare.

Share.

game da Author