Ortom, Mark sun yi wa Kwamishinan Zaben jihar Benuwai diran mikiya a ofis

0

A yammacin Lahadi ne Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom da tsohon shugaban majalisar Dattawa, David Mark suka yi wa ofishin da ake tattara sakamakon zabe dake garin Makurdi diran mikiya.

Diran su ke da wuya sai suka zarce kai tsaye zuwa ofishin Kwamishinan Zabe na jihar, Nentawe Yiltwada.

Ba a dai bayyana dalilin halartar su wannan ofis ba sai dai akwai rade-radin cewa sun zo ne su shaida wa shi kwamishinan zabe na jihar wannan ofis cewa wasu sojoji sun tare masu tattara zabe inda suka yi awon gaba da takardar sakamakon zabe na wasu yankunan jihar.

Share.

game da Author