Jim kadan bayan kadsa kuri’arsa a garin Daura, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa manema labarai da suka tambaye shi ko zai mika mulki idan bai yi nasasa ba, Buhari ya masa musu da cewa ” Ai nine zan lashe zaben shugaban kasa ko tantama bashi da shi.
Shugaba Buhari da mai dakin sa Aisha Buhari sun kada kuri’un su ne a rumfar zabe dake garin Daura.
Idan ba a manta ba a jiya Juma’a ne Jirgin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dira a garin Katsina ranar Juma’a da rana.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari da wasu Sanatoci ne suka tarbe sa a filin jirgi na Katsina Inda bayan ‘yar kwarya-kwaryar maraba da aka yi masa sai ya zarce garin Daura.
Bayannan ya yabwa yadda ake gudanar da zabukan bisa ga rahotannin da yake ta samu.
Discussion about this post