NASARAR ZABE: Kada magoya baya na su tozarta masu adawa da ni –Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabin godiyar sake samun nasarar zama shugaban kasa karo na biyu, bayann sanarwar yinn nasara da INEC ta yi da asubahin yau Laraba.

A cikin jawabin, Buhari ya gode wa daukacin ‘yan Najeriya, kuma ya gode wa musamman Jigon APC Bola Tinubu, Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole da Daraktan Kamfen, Rotimi Ameachi.

Shugaba Buhari ya kuma gode wa dimbim jama’ar da suka bayar da gudummawa a lokacin kamfen din sa a fadin kasar nan.

Sannan kuma ya gode wa wadanda suka sadaukar da kan su da lokutan su da dukiyoyin su wajen tabbatar da ganin an gudanar zaben cikin nasara.

Ya ce duk da cewa an gudanar da zabe lafiya, an samu tashe-tsahen hankula wasu wurare jifa-jifa, inda wasu batagari suka tayar da fitintinu.

Ya ce za a hukunta duk wanda ke da hannu wajen tayar da zaune tsaye a lokacin zabe.

Buhari ya nuna takaici da bacinn rai ganin yadda wasu suka rasa rayukan su sanadiyyar wannan zabe. Sai ya sha alwashin cewa za a kara tabbatar da jami’an tsaro sun karfafa kare lafiyar jama’a a zabubbuka masu zuwa.

Ya gode wa jami’an tsaro da masu sa-ido na gida da wadanda suka zo daga kasashen waje.

Sannan kuma ya sha alwashin ci gaba da karfafa inganta tattakin arziki, yaki da rashawa da magance matsalar tsaro a fain kasar nan.

A karshe ya ja kunnen magoya bayan sa kada murnar cin zabe ta sa su rika tozarta ‘yan adawa.

Share.

game da Author