Ministan Yada Lanarai, Lai Mohammed, ya kara yin ikirarin cewa tuni an kakkabe Boko Haram a Arewa maso Gabas.
Ya ce yakin da Najeriya ta tsinci kan ta a ciki yanzu, yaki ne da kungiyoyin ta’addanci na duniya su ka yi gangami da taron dangi a wuri daya a Arewa maso Gabas da yankin Tafkin Chadi.
“Lokacin da wani bangare na Boko Haram ya balle, sai suka yi mubayi’a ga kungiyar ta’addancin ISIS da ke Iraq da Syria. Daga nan sai suka kafa ISWAP, wato Kungiyar Jaddada Shari’ar Musulunci a Afrika ta Yamma. Ku ma suka zo suka yi kaka-gida a nan Najeriya.” Inji Lai.
“Da spjojin taron dangi ciki har da Amurka suka fatattaki ISIS daga Iraq da Syria, sai suka kwararo tare da makaman su zuwa nan Afrika ta Yamma, musamman Najeriya.
” Kuma a lura da cewa a can kafin a ci karfin su, sai da aka hada gangamin sojojin Amurka. Mu kuma da mu ke ta fama da su a yanzu, ba mu da agajin gangamin ko daga ita Amurka din.”
Lai ya yi wadannan jawabai ne jiya Alhamis a wurin kaddamar da Shirin Goyon Bayan Sojojin da ke bakin daga.
Ya kara da cewa sojojin Najeriya na matukar bukatar samun karin kwarin guiwa daga jama’a. B su so wasu sare musu guiwa ko yunkurin aibata su ta hanyar watsa labarai na karairayi.
Discussion about this post