Mai Girma Gamman Jihar Jiya Alhaji Badaru Abubakar na daya daga cikin gwamnonin da ke neman ci gaba da mulki a zaben 2019 da za a gudanar a ranar 2 Ga Faburairu.
Tuni gwamnan ya fara rangadin neman sake zaben sa kuma alamomi na nuna cewa Mai Girma Gwamna ya na kan nasara.
Idan mu ka yi duba da irin gaharimar tarba da ke samu a Kananan Hukumomi da kuma ziyarar da Shugaban Kasa Mujammadu Buhari ya kawo a Jigawa, za a gane cewa lallai Jigawa ta APC ce.
A ci gaba da yakin neman zaben sa karo na biyu da aka fara a kananan Hukumomin Guri da Hadejia, jirgin yakin neman zaben Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya ziyarci kananan Hukumomin Gagarawa da Gumel.
Jirgin yakin neman zaben gwamnan ya fara yada zango a karamar Hukumar Gagarawa inda babban Daraktan yakin neman zaben Gwamnan Alhaji Ahmed Mahmud ya bukaci al’umar karamar Hukumar Gagarawa da su fito kwansu da kwarkwatan su a lokacin zabe domin zaɓan ƴan takarar Jam’iyyar APC baki daya.
Ya ce sake zaben Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa shi zai bada damar cigaba da aiwatar da ayyukan raya kasa da aka faro.
A jawabinsa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya ce an kafa kamfanin Mr. Lee ne a garin Gagarawa domin bunkasa tattalin arzikin al’umar yankin.
Ya bukaci al’umar yankin da su zabi Jam’iyyar APC tun daga sama har kasa, kuma duk wanda ya ki yin hakan ba dan Jam’iyya ba ne.
Daga nan ne, jirgin yakin neman zaben, ya zarce zuwa garin Gumel inda a nan ne aka raba tutoci ga dan takara.
A Ƙaramar Hukumar Gumel kuwa gwamna Badaru Abubakar ya nuna jin dadi da kuma irin tarbar da aka masa inda ya bayyana cewar taron ya ƙayatar da shi.
Ya ce shugaban kasa Muhamamd Buhari ya cika alkawarin da ya yi wa yan Nigeria guda uku.
Sauran wadanda suka yi jawabai sun haɗar da shugaban Jam’iyyar APC na jiha Alhaji Ado Sani Kiri, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu, da Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan na Yankin Arewa maso Yamma Alhaji Isa Muhammad Gerawa.
Gwamna ya kuma gode wa sauran al’mmar Kananan Hukumomin da duk ya ziyarta, tare da fatan a zaben shugaban kasa, majalisa da na gwamna duk za a yi APC sak a jihar Jigawa baki daya.
Sako Daga: Auwal D. Sankara (Fica), Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa