Na san za a rina, dama can Hukumar Zabe bata shirya ba, ana rufa-rufa ne -Inji Balarabe Musa

0

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Balarabe Musa ya bayyana cewa kwata-kwata bai yi mamakin dage zabe da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi ba sai dai kawai abin bai yi masa dadi bane.

Balarabe Musa ya fadi haka ne da yake tattaunawa da wakilan Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya bayan an dage zaben ranar Asabar a Kaduna.

Ya ce rashin Kudi na daga cikin dalilan da ya sa aka dage wannan Zabe.

” Sanin kowa ne cewa kudaden da gwamnati ta ba Hukumar zabe, INEC, ba zai ishe ta ba da hakan zai sa dole ta yi fama da matsalolin gaske musamman na jigilan kayan Zabe zuwa garuruwa.

Baya ga haka Musa ya kuma ce akwai matsalar rashin tsaro da wasu sassan kasar nan ke fama da su Wanda ko da anyi zaben za a iya samun matsala a ire-iren wadannan wurare.

” Sannan ita kanta sashen shari’a na kasar da itama zata taka muhimmiyar rawa a zabukan a cukukkuye take da matsaloli ta ko-ina.

Tsohon gwamnan yayi Kira ga masu ruwa da tsaki da su yi maza-maza su kawo wa hukumar dauki na gaggawa domin a samu a iya yin zaben cikin kwanciyar hankali. Sannan ya roki ‘yan Najeriya da su ci gaba da hakuri sannan su kwantar da hankulan su, ayi fatan ayi Zabe lafiya a sabbin ranakun da hukumar ta sanar.

Hukumar zabe ta sanar da dage zabukan shugaban kasa da na majalisar kasa daga 16 zuwa 23 ga Fabrairu. Za ayi zaben gwamnoni da na majalisar jiha ranar 9 ga watan Maris.

Share.

game da Author