Mutane biyu sun mutu a arangamar PDP da APC a jihar Kano–‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa a dalilin arangamar da aka yi tsakanin wasu magoya bayan jam’iyyun APC da PDP mutane biyu sun mutu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a garin Kano.

Haruna yace wannan abin tashin hankalin ya auku ne a ranar Alhamis da karfe biyu na rana a Kofa dake karamar hukumar Bebeji.

Ya ce a dalilin wannan rikicin an kona motoci 20,an bata wasu guda 18 kuma sannan an kona wata cibiyar kiwon lafiya.

Haruna yace tuni rundunar ta kama wasu mutane 20 da ake zargi suna da hannu wajen tada rikicin. Sannan rundunar ta ja kunnuwar mutane da su nisanta kan su daga tada rikici a jihar musamman a wannan lokaci na zabe.

Bayanai sun nuna cewa wannan rikicin ya barke ne a lokacin da tsohon gwamnan jihar Rabi’u Kwankwaso da dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP Abba Kabir-Yusuf ke hanyar su ta zuwa karamar hukumar Bebeji domin gudanar da taron rufe kamfe.

Share.

game da Author