A yau Alhamis ne shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) Mahmood Yakubu ya sanar cewa hukumar zabe ta dauki wasu matakai domin ganin zaben gwamnoni da majalisar dokoki na jiha da za a yi ranar 9 ga watan Maris ya gudana yadda ya kamata.
Yakubu ya sanar da haka ne a hedikwatar hukumar dake Abuja a wata zama da ya yi da jami’an hukumar na jihohi.
Ya ce za a yi zaben gwamnoni da na majalisar dokoki na jiha a jihohi 29 ne kawai.
Yakubu ya kuma kara da cewa za kuma a yi zaben shugabanin kananan hukumomi da kansiloli duk a wannan ranar.
Ya ce hukumar ta yi wannan zama ne domin ganin yadda za ta kauce wa matsaloli a lokacin zabe ta hayar kawar da matsalolin da aka yi fama da su a lokacin zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki na kasa.
” Hakan zai taimaka mana wajen inganta shirin zaben da zai gudana a nan gaba.
Yakubu yace bayan sun kammala wannan zama hukumar za ta sanar da matakan da suka dauka domin samun nasara a zabukan dake tafe.
Discussion about this post