Mu dauki rashin nasarar PDP a Kano a matsayin Kaddara, Kada a tada hankalin jama’a – Inji Kwankwaso

0

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya roki magoya bayan sa da na jam’iyyar PDP da su kwantar da hankulan su su zauna lafiya a jihar.

Kwankwaso yayi wannan kira ne bayan an bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da akayi na jihar inda jam’iyyar PDP tayi gagarimin rashin nasara.

Bayan tika Atiku da APC ta Buhari ta yi da kasa, APC ce ta lashe duka kujerun majalisar dattawa na jihar.

Hakan yasa ana dan samun zaman dar-dara a tsakanin magoya bayan jam’iyyar da jam’iyyar Adawa.

Kwankwaso ya fito karar a tashohin radiyo na jihar Kano inda ya rika rokon magoya bayan sa da su dauki wannan nasara da APC ta yi a matsayin Kaddara daga Allah.

Duka da wannan kira da Kwankwaso yayi, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano Rabiu Bichi ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta amince da sakamakon zaben da aka fitar daga jijhar ba saboda anyi wa jam’iyyar magudi.

Ko da yake shima Kwankwaso ya bayyana rashin jin dadin sa ga yadda aka rika yi wa jam’iyyar Adawa ta PDP murdiya a wasu wurare da dama a jihar a lokacin zaben shugaban kasa da akayi a karshen makon da ta gabata.

Bayannan Kwankwaso ya roki mutanen jihar musamman magoya bayan sa dasu ci gaba da shiri domin akwai zaben gwamna dake tafe.

” Ina kiran ku da kara shiri domin tunkarar zaben da ke tafe, wato zaben gwamna da za ayi nan da mako daya mai zuwa.”

Share.

game da Author