Ministan Shari’a da Oshiomhole sun ce INEC ta gaggauta wanke ‘yan takarar APC na Zamfara

0

Yayin da jiya Laraba Kotun Daukaka Kasa a Abuja ta ce INEC ta yi daidai da ta ki amsar ‘yan takarar APC na jihar Zmafara, saboda ba su yi zabe a kan lokacin ba, sai kuma ga wata takarda da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya rubuta wa INEC inda ya nemi ta amince da sunayen ‘yan takarar APC a zabukan Jihar Zamfara.

Malami dai ya rubuta wasikar a ranar Laraba, 13 Ga Fabrairu, kuma shi da kan sa ya sa mata hannu.

A wata sabuwa kuma, shi ma Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya rubuta wa INEC wasika a rana daya da ta Minista Malami cewa INEC din ta karbi sunayen ‘yan takarar APC daga jihar Zamfara.

Sai dai kuma ba a sani ba ko wasikun sun kai hannun INEC. Wasu makusantan Malami ne da Oshimhole suka watsa wasikiun guda biyu da aka rubuta a rana daya, ranar da Kotun Daukaka Kara ta ce INEC ta yi daidai da ta ki karbar sunayen na su.

A cikin ta sa wasikar, Malami ya kuma nemi INEC ta kara wa jihar Zamfara wa’adi domin jam’iyyar APC ta “kara shiri”.

Ministan ya ce ya bada wannan shawara ce a bisa hujjar Sashe na 8 da na 39 na Dokar Zabe ta Kasa.

Ya kuma kara bada misali da abin da ya faru a Kotun Daukaka Kara ta Sokoto.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta tantance abin da ya faru a Sokoto, cewa Kotun Daukaka Kara ta Sokoto, ba ta ce INEC ta karbi sunayen ba.

Abin da kawai kotun ta yi, shi ne korar karar ta yi, bayan wanda ya kai karar yace ya janye kara, ba ya ja da Kotun Tarayya ta Abuja wadda a makon da ya gabata ta jaddada hukuncin Babbar Kotun Tarayya, ta ce ba a yi zaben ‘yan takarar APC a Zamfara ba.

Share.

game da Author