Mazabar El-Rufai ta yi wa Buhari ambaliyar kuri’u

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai sai da ya Kai har kusan karfe 10 na dare domin ganin an kirga kuri’u a gaban sa ranar Asabar, burin sa ya cika kuwa domin Buhari ne ya lashe Zabe a wannan mazaba.

Duk da cewa sai bayan ya tafi gida ne aka iya Kai wa ga Kammala wawware kuri’un da aka kirga kuwa Buhari ne ya lashe zaben wannan mazaba.

Buhari ya tashi da kuri’u 371 sannan shi Kuma Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’u.

El-Rufai sai da yayi awa hudu cur a Kan layi kafin a ka kai kansa ya kada kuri’a.

Har zuwa yanzu ana ta aikin tattara kuri’u a fadin Jihar.

Share.

game da Author