Likitoci sun bayyana cewa bakaken fata Yan Kasashen Afrika sun fi fama da cutar dajin dake Kama marainai.
Likitoci sun fadi haka ne a taron samun madafa game da cutar da aka yi a Abuja a makon da ta gabata.
Jagoran binciken Oseremen Aisuodione-Shadrach ya ce za su gwada maza 3800 dake dauke da cutar da maza 3800 da basa dauke da cutar dake kasashen Afrika.
Cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina cuta ce dake kama ‘ya’yan marainan namiji inda a dalilin haka baya kan iya yin fitsari yadda ya kamata. Sannan cutar ya fi kama maza masu shekaru 40 zuwa sama.
Bincike ya nuna cewa wannan cutar na daya daga cikin cututtukan dake yawan kisan maza a duniya.
Alamun wannan cutar sun hada da rashin iya yin fitsari yadda ya kamata,yin fitsari da jini,ciwon kirji da sauran su.
Likitoci sun bayyana cewa shan taba,shan giya na kawo cutar sannan ma aka iya gaji cutar.
Za a iya guje wa kamuwa da wannan cutar ne idan ana zuwa asibiti domin yin gwajin cutar sau daya a shekara domin gano cutar da wuri na cikin hanyoyin hana yaduwarta da samu warkewa.
Cin kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa na taimakawa wajen kare mutum daga kamuwa da cutar.
Abubuwa 8 da ya kamata a sani game da dajin dake kama ‘ya’yan marainai.
1. Cutar ya fi kama bakaken fata maza a duniya.
2. Ana iya gadon cutar.
3. Cutar baya hana karfin mazakutan namiji.
4. Zuwa asibiti domin yin gwajin cutar na cikin hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
5. Cutar ya fi kama maza daga shekaru 40 zuwa sama.
6. Rashin iya fitsari da yin fitsari da jini na cikin alamun cutar.
7. Shan tabar sigari, giya na iya kawo cutar.
8. Cin ‘ya’yan itatuwa kamar su tufa da ganyayakin da ake ci na hana kamuwa da cutar.
Discussion about this post