Kungiyar bin-diddigin gudanar da zabe sahihi, wato wato YIAGA da ta ‘Not Too Young To Run’, sun bayyana cewa matasa 1,155 ne suka fito talarar mukamai a siyasa na daban-daban.
YIAGA ta ce wadannan matasa su na cikin rukunin wadanda suka fara daga shekara 18 zuwa 35.
Daraktar YIAGA, Cynthia Mbamalu, ta bayyana cewa sun tsamo wannan adadi na matasa ne daga jerin sunayen da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar.
Sunayen dai na kunshe har da adadin shekarun kowane dan takara, wadanda 1,155 matasa ne masu takarar kujerun sanata da kuma majalisar tarayya.
Wakilai daga kungiyar USAID, Bea Reaud, UKAID da kuma na Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), duk sun halarci taron.