Matakai 5 da INEC ta dauka kafin sabuwar ranar zabe

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana sabbin matakai har 5 da ta ce ta duka domin magance matsaloli da kalubalen da da ta fuskanta kafin ta daga zabe.

INEC ta ce za ta tabbatar da ta magance matsalolin da kalubalen kafin nan da zuwan sabuwar ranar da ta bayyana cewa za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa, wato ranar 23 Ga Fabrairu, 2019.

Da ya ke lissafa su dalla-dalla, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce wadannnan matakai su ne za su zama sha-yanzu-magani-yanzu na matsaloli ko kalubalen da aka fuskanta a baya.

Matakan sun hada da:

1 – Fabrairu 17-21: Za a sake saisaita Na’urar Tantance Mai Zabe. Wannan ya zama tilas saboda kafin a dage zaben, an saita na’urorin ne yadda a ranar zabe, 16 Ga Fabrairu ne kadai za a iya sarrafa su. Kenan yanzu sai an saita su, zuwa ranar 23 Ga Fabrairu.

2 – Fabarairu 18: Za a kammala saitata da tantance kayan zabe.

3 – Fabrairu 20 – 21: za a rarraba kayan zabe a Kananan Hukumomi.

4 – Fabrairu 21: Za a yi wa ma’aikatan zabe na wucin gadi wani dan kwarya kwaryan bitar sanin makamar aiki.

5 – Fabrairu 22: Tura jami’an zabe a Cibiyoyin Yin Zabe daban-daban.

INEC ta kuma bada hakuri ga ‘yan Najeriya da dukkan masu ruwa da tsaki tare da neman su fahimci halin da ya tilasta dage zaben.

Share.

game da Author