Masu garkuwa da mutane sun sace dakacen wani kauye a jihar Nasarawa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun sace Yakubu Dauda dakacen kauyen Gida-Barkin Kogi dake karamar hukumar Lafia.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Samaila Usman ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Lafia.

Usman ya ce masu garkuwan sun sace Dauda a cikin gidan sa ne da karfe 1:25 na safiyar Litini.

” Masu garkuwan sun harba bindiga a sama bayan sun kama Dauda domin hana mutane kawo masa dauki sannan suka yi daji da shi.

Usman ya ce tuni rundunar ta hada hannu da ‘yan banga da masu farauta dake kauyen domin taso keyan masu garkuwan da ceto dakacin.

Ya kuma ce rundunar ta kafa jami’an tsaro domin samar da tsaro a kauyen Gida-Barkin Kogi, Assakio, Obi da Lafia.

Share.

game da Author