Wani mai gadin ofishin Hukumar Zabe da ke Karamar Hukumar Qua’an Pam a Jihar Filato, ya banka wa ofishin wuta, har dukkan kayan zaben da ke ciki gaba daya suka kone kurmus.
Babban Jami’in Wayar da Kai na INEC a Jihar Filato, Osaretin Imajiyereobo, ya tabbatar da cewa wani mai gadin ofishin ne ya banka masa wuta bayan ya yi mankas da giya.
Daga cikin kayan da suka kone kurmus, akwai dukkan akwatunan zaben da za a yi amfani da su, tulin katin rajista na dindindin da masu su ba su kai ga karba ba, rajistar da ke dauke da sunayen masu zabe na karamar hukumar da ke kan takarda da kuma na cikin kwamfuta.
Jami’in ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa zuwa lokacin da ta ke hada wannan labarin, ba a tantance wane mai gadin ba ne.
Wannan gobara ta maida wa aikin INEC hannun agogo baya, a sha’anin gudanar da zabe a Karamar Hukumar Qua’an Pam.
Wannan karamar hukuma ta na daya daga cikin kananan hukumomi shida da suka kunshi shiyyar sanatan Filato ta Kudu.