Dan takarar jam’iyyar APC, Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasara a kan Atiku Abubakar na PDP a jihar Lagos, da tazarar kuri’u 132,810 kacal.
Buhari ya yi nasara a kananan hukumomi 15, shi kuma Atiku ya shige gaba a kananan hukumomi 5 kacal.
Buhari ya samu kuri’u 580,825, shi kuma Atiku ya samu 448,015.
An yi ta sa ran Buhari zai samu kuri’u masu dimbin yawa, ganin yadda al’amurran ayyukan gwamnatin sa ya fi karkata a jihar Legas.
Sannan kuma da ya ke jigon APC, Bola Tinubu a Legas ya ke, haka Ministan Ayyuka, Makamashi da Gidaje, Raji Fashola shi ma a Legas ya ke, an yi tunanin APC za ta samu kuri’u masu yawa, sama da Katsina da Kano.
Idan ba a manta ba, a lokacin da ake tsakiyar kamfen, Tinubu ya bugi kirjin cewa Jihar Lagos za ta samar wa Buhari kuri’u miliyan uku.
Sama mutum milyan biyar ya yanki rajistar zabe a jihar Lagos. Amma wadanda suka fito suka jefa kuri’a kadan suka gota milyan daya.
Discussion about this post