Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana cewa furcin gwamnan jihar Kaduna cewa cewa duk wani dan kasar waje da ya yi wa Najeriya katsalandan a harkar zabe mai zuwa za a kai gawar sa ne gida ba shi ba bai bata tada mata da hankali ba.
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Najeriya ba za ta zuba ido ta bari wani daga kasan waje ya zo kasarnan ya saka mata baki a harkokin ta ba musamman a wannan lokaci na zabe cewa duk wanda yayi haka toh lallai ko za a koma da gawar sa ne gida.
Gwamna El-Rufai, wanda dan jam’iyyar APC ne mai mulki, ya na a sahun gaban masu goyon bayan Buhari na karshe, ya caccaki jam’iyyun adawa da kungiyoyin kasa da kasa masu sa-ido kan zabe.
Ya yi caccakar ce a wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na NTA a jiya Talata da dare, a wani shiri mai suna ‘Tuesday Live’. Cyril Stober ne ya tattauna da shi.
“Masu kiran wasu su shigo su sa-baki cikin harkokin Najerya, to a fada musu mu na jiran mu ga duk wanda zai shigo ya yi mana katsalandan. Wanda ya kuskura ya shigo, to sai dai a maida gawarwakin su a cikin buhunan daukar gawarwaki can a kasashen da suka fito.”
Kungiyar EU ta ce ba tun yanzu ba ne ta fara kula da yadda ake zabe a kasar nan ba. Kungiyar tace tun a shekarar 2019 ta fara wannan aiki kuma za ko a zaben bana ma gwamnatin kasar ce ta gayyace su yin haka saboda haka za ta yi aikin ta ba tare da tsoro ba.
” Abu daya da za mu fi mai da hankali a kai shine tsaron ma’aikatan mu. Lallai zamu tabbata sun samu tsaro yadda ya kamata. Sannan kuma mu iyakan mu ba da rahoton yadda zabe ya guda a inda muke da wakili amma babu abinda za mu yi da ya wuce haka.