A yau Litinin ne kotu dake jihar Kano ta bada belin Mai rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju bayan ya yi kwanaki 67 a daure.
Theophilus Agada lauyan dake kare Adeyanju ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa kotun ta yardan wa Adeyanju ya tafi gida idan har ya iya cika sharuddan belin da kotun ta yanke masa.
Wadannan sharrudda sun hada da gabatar da shaida wanda babban ma’aikaci ne a gwamnatin jihar Kano, takardun manyan filaye biyu sannan da Naira 500,000.
” Muna sa ran cewa kotu za ta saki Adeyanju yau domin zai iya cika wadannan sharruddu da kotu ta bada.” inji Agada.
Idan ba a manta ba Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana tsare dan taratsin kare hakkin jama’a, Deji Adeyanju a kurkuku da cewa tuggu da sharrin siyasa ne, ba matakin shari’a ba.
Saraki ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta bada umarnin a saki Adeyanju, domin ya tabbatar da cewa bai kyale ‘yan sanda na ci gaba da danne wa Adeyanju hakkin sa na ‘yancin dan adam da ‘yan sanda suka tauye ba.
Wannan kakkausan kira da Saraki ya zo ne kwanaki shida bayan da majalisar dattawa ta bai wa Kwamitin Majalisa kan Shari’a da Harkokin ‘Yan Sanda mako daya da ya gudanar da bincike kuma ya gano kwamacalar da ta haddasa ‘yan sanda kama Adeyanju har su kai shi Kano a kotu, daga can kuma a zarce da shi kurkuku.
An fara kama shi a ranar 28 Ga Nuwamba, bayan da ya ja zugar masu zanga-zanga a kan nuna fushi da damuwa dangane da yadda manyan shugabannin tsaron kasar nan ke nuna bambanci da son kai a lamurra da batutuwan zabe mai zuwa na 2019.
Bayan an bayar da Belin sa a ranar 6 Ga Disamba, sai ‘yan sanda suka sake kama shi a kofar kurkukun Keffi, daidai lokacin da ya fito.
An garzaya da shi kotu a Kano a bisa wani abin da ‘yan sanda suka kira sabon binciken da ya taso dangane da wata shari’ar zargin kisa da aka taba yi wa su Deji Adeyanju, wanda aka yi tun lokacin da ya ke karatu a Jami’ar Bayero, Kano.
Idan ba a manta ba, jim kadan bayan kama Deji, lauyan sa a lokacin da aka yi waccan shari’ar, Festus Kiyamo ya fito ya ce Deji ba shi da laifi, kuma a wancan lokacin ma alkali ya wanke, shi ba a same shi da laifi ba.
Keyamo ya yi wannan furucin ne duk kuma da cewa a yanzu ya na cikin gwamnatin Buhari.
A yanzu dai a na tsare da Adeyanju ne sai cikin watan Fabrairu za a yi maganar beli, domin alkali su na hutun karshen shekara.