KOFIN ZAKARUN TURAI: Yadda ta kaya a wasannin zagaye na biyu

0

Kamar yadda aka sani ne, a gasar cin kofin Zakarun Turai wato Champions League, duk kungiyar da ta kai zagaye na biyu, to sai da ta sha fafatawa da kungiyoyi kafin ta kai ga saura 16 da suka rage daga cikin 32 din da suka fafata.

To sai dai kuma a Zagaye na Biyu ne ake fara yin gudun yada kanin wani, inda gwanaye kadai ke iya zarcewa zuwa zagaye na uku.

A wasannin zagaye na biyu da aka buga ranakun Talata da Laraba. Ta fara nuna wadanda za a iya cewa ba za su kai labari ba. Ko da yake dai sau da dama ba a nan ta ke ba.

MANCHESTER vs PSG

An je har gidan Manchester an lakada mata duka da ci 0:2. Wannan nasara ita ce ta farko da aka yi a kan kungiyar tun daga lokacin da sabon mai horaswa, Ole Gunner Solkjear ya karbi ragamar kulob din daga hannun Jose Mourinho.

Ganin yadda PSG ke wasa kuma da karfin ta, sai yi wuyar gaske Manchester ta yi nasara a kan ta a birnin Faris idan ta kai mata ziyara, makonni biyu masu zuwa.

PSG ta so a ce ta kara jefa wa Manchester United kwallaye, duk kuwa da cewa fitattun ‘yan wasan ta biyu, Edison Cavani da Neymar ba su buga ba, saboda rauni.

ROMA vs FC PORTO

Roma ta daka wa Porto kwallaye 2:1 a birnin Rome, wadanda ake gani Porto za ta iya rike wa Roma wuya a birnin Lisbon. Amma dai sai an tashi za a san wanda zai iya yin nasara.

TOTTENHAM vs Dortmund

Kungiyar Tottenham ta yi bazata, inda ta lallasa Brussia Dortmund ta Jamus da ci 3:0.

Kowa ya yi tsammani za a yi wasan kura da Tottenham, ganin yadda ta ke ta samun rashin nasara a wasan ta na baya-bayan nan a Gasar Premier.

Dortmund ta na da karfi sosai, kuma ita ce kan gaba a gasar Bubdesliga na Jamus. Za ta iya ramawa kwallayen ta. Amma kuma ko kwallo daya Tottenham ta jefa mata a gida, to shirin Dortmund zai warware kenan.

AJAX vs REAL MADRID

An tashi wannan wasa 1:2 inda baki su ka yi nasara kan masu masaukin baki. Wannan zai ba Madrid karfin guiwa ganin cewa ta tsallaka zuwa gaba, bayan kafsawar da za ta sake yi da Ajax din a Santiago Barnabeau, Sifen.

Sai dai kuma wannan nasara ta haifar da ka-ce-na-ce, tun bayan da aka jefa wa Madrid kwallo a raga, amma daga baya na’urar raba-gardama ta ce an yi kwange kafin a doki kwallon ta shiga gidan Madrid.

Share.

game da Author