Ko me ya sa Gwamna Kashim Shettima ba ya saka sulke a jikin sa

0

Wata majiya ta jami’an tsaro ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa jami’an tsaron Gwamna Kashim Shettima na Barno su na shan fama da shi wajen shawo kan sa ya riga amfani da motoci masu sulken hana harsasai huda su, amma ba ya amincewa ya yi amfani da su din.

PREMIUM TIMES ta ji wannan bayanin ne kwana biyu bayan kwanton bauna da Boko Haram su ka yi wa tawagar gwamnan a ranar Talata da yamma, a kan hanyar tawagar ta sa ta zuwa Dikwa da Mafa yakin neman zabe.

Majiyar wadda ta ce don Allah a sakaya sunan ta, ta ce akwai motoci biyu masu sulke, wato ‘bullet proof’ a Gidan Gwamnati a Maiduguri, amma duk inda gwamnan zai tafi ba shi amfani da su.

Majiyar ta ce motocin sun a can ajiye sai dai idan an yi wasu mayan baki a jihar, sai a rika daukar su a cikin ta domin yin zirga-zirgar su.

Majiyar ta kara da cewa Shettima nada tsatstsauran ra’ayin cewa shi ya na ganin ba adalci ba ne shi ya shiga cikin mota mai sulke, alhali bakin sa ko hadiman da ke take masa baya sun a cikin motocin da sha yanzu magani yanzu za a iya bindige mutum a cikin su.

Ya na mai kaifin ra’ayin cewa idan duk inda za a je ya rika shiga shiga mota mai sulke, to zai rika sa sauran masu rakiyar fargabar cewa watakila shi gwamnan ya san akwai matsala kenan, shi ya say a yi shiri tun daga gida.

Majiyar ta ce an sha nuna wa gwamnan cewa a matsayin sa na gwamna, doka ta ba shi wata kariya ta musamman, kuma shi ne ma Boko Haram za su fi son su bindige ba sauran mukarraban sa ba.

Majiyar ta ce gwamnan ba shi da tsaro, kuma ba shi da fargabar komai, domin ko lokacin da Boko Haram suka kashe Sarkin Chibok da na Gwoza a cikin 2014, haka ya shiga mota har garuruwan, ba tare da shiga mai sulke ba.

Kwanan nan Gwamna Kashin ya je har garin Monguno ya kwana can, kwanaki kadan bayan da Boko Haram suka kai hare hare harasau uku a jere.
Majiyar ta ce, maimakon Shettima ya je ya kwana a cikin sansanin sojoji a cikin garin, dai ya yi kwanciyar sa a bangaren fararen hula da babu cikakken tsaro.

Daga nan sai majiyar PREMIUM TIMES ta ce ya kamata hukumar tsaro ta NSA ta nuna masa muhimmancin sa kula da lafiya da ran sa, a matsayin sa na gwamna.

PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda gwamna Shettima ya yi ta tankiya shi da sojojin da ke tsaron hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Gamboru-Ngala, bayan sojoji sun hana su wucewa zuwa kamfen a ranar Talata da yamma.

Sojoji sun yi kokarin hana su wucewa ne domin a ta bakin sojojin hanyar akwai hatsarin gaske, saboda Boko Haram na yawan kai farmaki.
An ce gwamnan ne da kan sa ya umarce su da su bude hanyar domin su wuce.

Bayan sun wuce wurin ne ba da nisa ba, Boko Haram suka yi musu kwanton bauna suka budewa tawagar wuta.

Da yake tawagar gwamna ta rigaya ta wuce, kafin a bude wa na baya wuta, gwamna ya zarce garuruwan da ya yi niyyar zuwa kamfen, kuma har kwana ya yi a can, sai jiya Laraba da yamma ya koma Maiduguri.

Share.

game da Author