KISAN KIYASHIN KAJURU: Za a Kamo duk wandanda suke da hannu a wannan kisa a hukunta su – Inji Buhari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin kakkausar murya ya yi tir da kisan kiyashin da aka yi wa wasu mazauna kauyukan karamar hukumar Kajuru ranar Juma’a.

Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta tabbata ta bi diddigin abin da ya faru sannan za ta hukunta duk Wanda aka samu da hannu a aikata wanna mummunar abu.

A jiya Juma’a Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan akalla mutane 66 a harin da aka kai wasu kauyukan kaeamar Hukumar Kajuru, jihar Kaduna.

Kauyukan da aka kai harin sun hada da Ruga Bahago, Ruga Daku, Ruga Ori, Ruga Haruna, Ruga Yukka Abubakar, Ruga Duni Kadiri, Ruga Shewuka da Ruga Shuaibu Yau.

Kakakin gwamna Nasir El-Rufai, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da aukuwar wannan abun tashin hankali a takarda da ya raba wa manema Labarai.

El-Rufai ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a aikata wannan mummunar abu.

Yayi kira ga mutanen just har Kaduna sa su kwantar da hankulan su cewa gwamnati ta tura karin jami’an tsaro zuwa yankin kuma tuni har an yi kame da dama.

An kai wannan hari ne a ranar Juma’a. Cikin wadanda aka kashe akwai yara kanana 22 da mata 12.

Share.

game da Author