KISAN KIYASHIN KAJURU: Ina kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo karshen rikice-rikicen jihar Kaduna – Isa Ashiru

0

Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar PDP Isah Ashiru ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta taso keyar Wanda aka samu da hannu wajen aikata mummunan kisan da aka yi wa mutanen wasu kauyukan Fulani har 8 sannan da hukunta su kamar yadda yake doka.

” Rashin tsaro ya zama babbar matsala a Jihar Kaduna yanzu da hakan ya ke neman ya tarwatsa Jihar idan ba an yi gaggawar gano inda barakar yake bane an dinke shi maza-maza. Wannan yana daga cikin Dalilin da ya sa na fito takara domin in ceto jihar daga wannan matsala.

” A yanzu dole ne a rika sara ana dubar bakin gatari domin bamu da jiha da ya wuce Kaduna sannan Allah ne ya shirya zaman mu tare a wuri daya. Dole sai mun Kai zuciya nesa matuka kafin mu iya kawo karshen wadannan matsaloli. Dole sai an samu gwamnati mai hangen nesa da zata rungumi kowa sannan ta zamanto ta na kwatanta gaskiya da adalci, daga nan ne za a iya samun zaman lafiya.

A karshe Ashiru ya yi adu’ar Allah ya ji Kan mutanen da suma rasu sannan Kuma Allah ya Kara Mana hakuri da zama da juna.

Akalla mata 12 ne, yara kanana 22 aka yi wa kisan gare dangi da wasu da dama.

Share.

game da Author