Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi karin haske dangane da dalilan da suka sa INEC ta dage zaben 2019 zuwa nan da mako daya.
Hukumar ta bayyana dage zaben ana saura sa’o’i shida a fara fita shirin jefa kuri’a a tsakar daden jiya Juma’a.
Ta bada dalilai na matsalar rarraba kayan zabe, amma ba ta yi wani karin bayani ba a lokacin.
A taron manema labarai da Yakubu ya kira a yau Asabar da rana, ya bayyana cewa “dama ba za a taba tunanin cew irin wannan gagarimin aikin raba kaya da aika jami’an aiki ba zai iya fuskantar matsaloli ba.”
Daga cikin dalilan da ya lissafa, akwai kalubalen yunkurin a yi wa zaben makrkashiya, har ya bada misali da gobarar da aka rika banka wa wasu ofisoshin INEC, rashin kai kayan zabe kan zabe kan lokaci da kuma rashin kyawon yanayi a wasu yankunan kasar nan.
Ya ce wutar da aka banka wa wasu ofisoshi ya kawo asarar wasu kayan zabe da suka hada da na’urar tantance mai zabe da kuma katin masu jefa kuri’a.
Amma kuma ya ce duk da wannan koma-baya da aka samu, INEC ta gaggauta maye gurbin wadanda suka kone.
“Yace da an ci gaba da jefa kuri’a, to da zai kasance wasu jihohi an yi zabe, a wasu jihohin kuma an samu tsaiko.
“Da mu ka ga mun fuskanci wannan gagarimar matsala, da farko mun yi tunanin cewa za mu iya magance kalubalen a cikin sa’o’i 24 kacal. Wato hakan na nufin ko a daga zaben zuwa washegari Lahadi, ranar 17 Ga Fabrairu, 2019.
“To sai kuma mu ka ga cewa idan aka hana zirga-zirga a ranar Lahadi, hakan zai hana masu zuwa coci damar zuwa yin ibadar su.
“Mu na cikin wannan wasiwasin, sai bangaren kula da sarrafa na’urorin mu ya ce tilas sai an ba shi kwanaki 5 zuwa 6 domin ya sake jerawa da saisaita na’urar tantance katin kuri’a har guda 180,000. Domin a yadda aka tsara ta, babu yadda za a yi su yi aiki sai a ranar Asabar, 16 Ga Fabrairu, 2019 kadai.”
Yakubu ya ce tuni INEC duk ta tattaro kayan zaben da aka fara rarrabawa yanzu duk su na hannun ta, a ofisoshin ta.