Karfafa dokar hana siyar da taba sigari a Najeriya ne mafita ga matsalolin shaye-shaye da matasa ke fama da su

0

Kungiyoyin kiyayewa, fadakarwa da kare hakkin mutane sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta maida hanklai wajen tabbatar da dokar hana siyar da taba sigari a kasar.

Kungiyoyin sun yi wannan kira ne a taron gabatar da sakamakon binciken da kungiyoyin Gatefield, Campaign for Tobacco Free Kids (CTFK) da National Tobacco Control Alliance (NTCA) suka gudanar kan siyarwa da amfani da taba sigari a jihohi uku da Babbaban birnin tarayya, Abuja.

Wadannan jihohi kuwa sun hada da Katsina, Ekiti da Edo.

Biniciken ya nuna cewa kashi 15.4 bisa 100 na mutanen Najeriya (Maza da mata) na ta’ammali da taba sigari sannan kashi 89 bisa 100 na matasa ‘yan shekara 18 ne suka fi siyan ta, wato amfani da ita.

Sakamakon binciken ya nuna cewa babban birnin tarayya Abuja ta fi yin kaurin suna wajen yawan masu zukar taba sannan jihohin Ekiti, Katsina da Edo.

Idan ba a manta ba a 2015 ne gwamnatin Najeriya ta kafa dokar hana siyar da taba sigari musamman wa matasa ‘yan kasa da shekara 18.

Dokar ta kuma hana matasa irin haka yin tallar sigarin da tallata ta a gidajen talabijin da radiyo na kasar nan.

Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya Abraham Agboms ya bayyana cewa mafi yawa da ga cikin wadanda suke siyar da tabar basu san da wannan doka ba

Agboms ya ce ma’aikatar su za ta kara zage damtse wajen ganin ta wayar da kan mutane game illolin dake tattare da zukar taba sigari.

A karshe jami’in hukumar SON Batho Ugwu yace hukumar su a shirye take domin hada hannu da gwamnati wajen ganin an kawar da wannan matsalar a kasar.

Ya ce ba taba sigari ba har da tabar shisha hukumar su za ta dauki matakin gaske wajen hana amfani da su a kasar nan.

Share.

game da Author