KALAMAN EL-RUFAI: Gwamnati za ta ba masu sa-ido daga kasashen waje Kariya ta musamman – Fadar shugaban kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta saka baki dangane da kasassabar da Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi, inda ya furta cewa duk bakin da suka shigo daga kasashen ketare suka yi wa Najeriya katsalandan, za a maida gawarwakin su gida.

Gwamnan ya sha caccaka daga ko’ina a fadin kasar nan da kasashen ketare, duk kuwa daga baya ya fito ya yi wa furucin na sa kwaskwarima.

Ganin haka sai Fadar Shugaba Buhari ta yi gaggawar turo wa PREMIUM TIMES wata sanarwa a yau Alhamis inda ta yi karin haske.

Sakon wanda kakakin yada labaran fadar, Garba Shehu ya turo ta akwatin sako na yanar gizo, ya nuna cewa Najeriya na sanar da dukkan masu sa-ido daga kasashen waje cewa za a ba su dukkan kariya damar da ta dace su yi ayyukun su na sa-ido, ba tare da tsangwama ko tarnaki ba.

Sanarwar ta kuma kara jaddada cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi dukkan kokarin da karfin doka ya ba shi domin tabbatar da cewa an gudanar da zabe sahihi cikin lumana ba tare da magudi ba.

“ Mun yi karin haske dangane da kalamn da Gwamnan Kaduna, Nasir E-Rufai ya yi a matsayin raddi ga ‘yan adawa masu kiran kasashen waje su sa wa Najeriya baki a harkokin ta na cikin gida. Don haka wannan furuci na sa ya wuce, mun yi karin haske. Da fatan za a wuce wurin.” Inji Shehu.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya yi furucin ne a matsayin nuna kishi ga Najeriya, amma ba yekuwar neman tashin hankali ba ce.
Ta kara da cewa dukkan magoya bayan APC da dukkan masu yin takara a karkashin jam’iyyar mutane ne masu kishin kasar su da kuma dimokradiyya.

Sai dai kuma bayan wannan kalamai na El-Rufai ya karade duniya sai gwamnan ya yi karin haske kan abin da yake nufi da wadannan kalamai da yayi.

El-Rufai ya bayyana cewa ba a fahimci abin da yake nufi bane in da ya ce duk wanda ya yi wa kasa Najeriya katsalandan a harkokin zabe, yayi shirin zama gawa.

Ya kara da cewa abinda yake nufi shine kasa Najeriya ba za ta yarda wani ya shigo kasar nan ya yi mana katsalandan ba a harkokin mu amma ba wai yana kira bane da a yi tashin hankali ko kuma domin wanta manufa da ba na zaman lafiya ba

Share.

game da Author