Kada ku bi umarnin wadanda suka ce ku karya doka da sunan Buhari -Jakadan Amurka

0

Jakadan Amurka a Najeriya, Stuart Symington, ya gargadi jama’a cewa kada su sake su bi umarnin wasu jami’an da za su ce musu su karya doka domin su biya bukatar nasarar zabe da sunan Shugaba Muhammadu Buhari.

Symington ya yi wannan gargadin ne a jiya Alhamis a Makurdi, bayan ganawar sa Gwamnam Jihar Benuwai, Samuel Ortom.

Ya shaida wa ‘yan jarida haka a ganawar da ya yi da su.

Ya ce, “Idan suka zo suka ce ku karya doka domin umarni ne daga sama, to kada ku yarda da su. Domin abin da muka hakkake dai shi (Buhari) ya ce za a yi zabe mai adalci, kuma mun yi amanna da wannan kalami na sa.”

Gidan Talbijin na Channels ya ruwaito Jakadan na cewa ‘yan Najeriya su sani cewa farkon abin da ya wajaba a kan su, shi ne riko da igiyar Allah da tsoron Allah.

Ya ce daga nan sauran muhimman abubuwa irin su hankali da tunani, bin doka da sauran matakan dokoki kan biyo baya.

Ya yi wannan jawabi ne kwana biyu bayan Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi kasassabar cewa wadanda suka shigo kasar nan suka yi katsalandan, to za a koma da gawarwakin su a jakar zuba gawa.

Share.

game da Author