Sanata Kabiru Gaya da Jibrin Barau na jam’iyyar APC duk sun lashe zabukan mazabun su da aka yi ranar Asabar.
Gaya na Kano ta Kudu, ya samu kuri’u 319,004, Sani Rogo na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 217,520, Yahaya Karaye na PRP kuma da kuri’u 30,013.
A Kano ta Arewa kuma Jibrin na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 286,419 da ya kada Ahmad Bichi na jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u 155,638.
Discussion about this post