Jam’iyyu 44 sun saka hannu a takardar yarjejeniyyar zaman lafiya a jihar Barno

0

Akalla jam’iyyu 44 ne suka saka hannu a takardar yarjejeniyyar zaman lafiya a lokacin zabe a jihar Barno.

Wakilan jam’iyyun sun saka hannu kan wannan takarda ne a karkashin sa idon rundunar ‘yan sandan jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Damian Chukwu yace saka hannu a wannan takarda zai hada kan jam’iyyun da ‘yan takara.

Ya ce yin haka ya zama dole ganin cewa an yi ta kawo wa rundunar korafe-korafe game da tsoron barkewa da rikici a ranar zabe.

Chukwu ya kuma ce rundunar ta kafa rumfunar sauraren ire-iren wadannan korafe-korafe da kararrakin rikici a lokaci da bayan zabe.

Ya kuma yi kira ga ‘yan takara da jam’iyyu da su guji tada rikici a lokacin zabe yana mai cewa duk wanda aka kama zai dandana kudar sa.

A karshe shugaban IPAC Mukhtar Abdallah da jami’in NOA Yahaya Imam sun yi kira ga jam’iyyun kan girmama saka wannan hannu a takardar yarjejeniyyar zaman lafiyar da suka yi ta hanyar hada hannu da jami’an tsaro domin ganin zabe ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana a jihar.

Share.

game da Author