JAJIBIRIN ZABE: An kashe mutum biyu, an kone motocin INEC 13

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kone wasu motocin aikin zabe a wani rikici da ya barke a Karamar Hukumar Obot-Akara da ke cikin jihar Akwa Ibom.

Rikicin wanda ya barke a ranar Juma’ar da ta gabata, an ce motocin da aka lalata din an dauko su ne domin daukar kayan zabe daga hedikwatar INEC ta Uyo zuwa Obot-Akara.

Kwamishinan Zaben Jihar, Mike Igini ne ya tabbatar da haka.

Wani da ya kalli yadda rikicin ya barke, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kuma kashe mutane biyu yayin barkewar rikicin.

Wannan ya janyo aka matakan tsaro a Karamar Hukumar. Sai dai shi kuma Igini bai tabbatar da kisan mutane biyu din da PREMIUM TIMES ta bada labari daga wata majiya ba.

Amma dai ya tabbatar da kone motocin, wanda ya ce wasu batagarin magoya bayan wasu ‘yan siyasa ne suka kone motocin.

Majiyar ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa motocin harkar zabe har 13 ne aka banka wa wuta.

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Uyo, Igini ya kara da cewa INEC ba za ta taba yarda a rika yin bankaurar da aka rika yi a lokutan zabukan baya a jihar ba.

Ya ce kuma wasu baragurbin ‘yan siyasa ba za su taba zame wa INEC wata barazana a jihar ba.

“Wannan babbar barazana ce a ce ’yan siyasa ne ke kona motocin da za su dauki kayan zabe. Sun manta da cewa su ne fa suka fi amfana da cin moriyar dimokradiyya.

Duk da haka ya ce ba a kona kayan zabe ba. Kuma ya ce su ba su goyon bayan kowace jam’iyya a jihar Akwa Ibom, ba kuma za su kyale wani dan siyasa ya yi abin da ya ga dama a lokacin zabe ba.

Share.

game da Author