Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan akalla mutane 66 a harin da aka kai wasu kauyukan kaeamar Hukumar Kajuru, jihar Kaduna.
Kauyukan da aka kai harin sun hada da Ruga Bahago, Ruga Daku, Ruga Ori, Ruga Haruna, Ruga Yukka Abubakar, Ruga Duni Kadiri, Ruga Shewuka da Ruga Shuaibu Yau.
Kakakin gwamna Nasir El-Rufai, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da aukuwar wannan abun tashin hankali a takarda da ya raba wa manema Labarai.
El-Rufai ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a aikata wannan mummunar abu.
Yayi kira ga mutanen just har Kaduna sa su kwantar da hankulan su cewa gwamnati ta tura karin jami’an tsaro zuwa yankin kuma tuni har an yi kame da dama.
An kai wannan hari ne a ranar Juma’a. Cikin wadanda aka kashe akwai yara kanana 22 da mata 12.
Discussion about this post