Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Anambra (INEC) Uchekachukwu Ibe ya bayyana cewa hukumar ta tattance kungiyoyin sa ido na zabe 60 a jihar.
Ibe ya fadi haka ne a Awka bayan ya kammala tattaunawa da wakilan kungiyoyin sa ido da na jam’iyyu ranar Laraba.
Ya ce daga cikin kungiyoyi 60 din da za su sa ido a zabe wakilan su 3,156 ne za su yi aiki a lokacin zabe.
Ibe yace wakilan za su gudanar da aiyukkan su ne bisa ga dokoki da sharadun INEC.
” Zan jadadda cewa masu sa ido a zabe da na jam’iyyu basu da ikon yanke hukunci game da wani korafi da suke da shi ko kuma su sanar da sakamakon zabe domin wannan aiki ne dake karkashin ikon hukumar zabe.
Ibe ya kuma ce hukumar za ta fara raba wa wakilan kayan da za su yi amfani da shi a zaben da karfe tara na safiya daga yau Alhamis.
Wani jami’in INEC Charles Mbanaja yace kayan aikin zaben da suka kone a gobarar da ta auku a ofishin su ranar 12 ga watan Fabrairu bazai shafi zabe ba a jihar domin hukumar ta kawo sabbin kayan da za a yi amfani da su.
Ya kuma ce hukumar za ta fara jigilar ma’aikata da kayan zabe da wuri domin ganin cewa zabe ya fara a duk rumfunar zabe a jihar da karfe 7:30 na safe.
Discussion about this post