Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta gargadi jam’iyyun siyasa da su gaggauta mika mata sunayen ejan da za su wakilce su a zabukan gwamna da na majalisun jihohi.
Daraktan Wayar da Kai da Yada Labarai, Festus Okoye, ne ya bayyana haka. Ya kara da cewa daga ranar 16 Ga Fabrairu ba za a kara karbar sunayen ba ko da jam’iyya ta kai wa ofishin INEC.
Okoye, wanda ya bayyana haka a wata ganawa ta INEC ta yi da Kwamishinonin Zabe na Jihohi 36, ya kuma lissafa cewa za a hado da hotunan ejan guda biyu da kuma sa hannun sa a bayan kowane photo tare da cikakken sunan sa.
INEC ta kuma ce babban laifi ne a kama wani ya na yi wa wata jam’iyya ejan ba tare da INEC ta tantance sunan sa ba.
Dokar INEC ta Sashe na 45 (1) na 2010, ya rattaba cewa kowace jam’iyya ta aika wa INEC sunayen ejan din ka kafin kwanaki 14 ranar zabe ta zo.