Shugaban hukumar zabe INEC Mahmoud Yakubu ya bayyana cewa hukumar ta kara yawan kwanakin karban katin zabe.
Yakubu ya sanar da haka ne da yake ganawa da wasu jami’an hukumar a Abuja ranar Juma’a.
Ya ce hukumar ta kara yawan kwanakin daga ranar Juma’a 8 ga watan Faburairu zuwa Litini 11 ga watan Faburairu.
Yakubu ya ce hukumar ta yanke hukuncin haka ne a dalilin kiraye-kiraye da jihohin kasar nan da dama ke yi cewa mutane burjik basu karbi katin zaben su ba. Jam’iyyar PDP tayi irin wannan kuka.
Domin ganin kowa ya karbi katin sa ne Hukumar ta kara yawan rufunan karbar katin Zaben da kuma ranakun da za aba da katin.
Za a yi zaben shugaban kasa a ranar 16 ga watan Faburairu sannan za a gudanar da zaben gwamnoni ranar 2 ga watan Maris.