Kwamishiniyar Zabe dake Kula da shiyyar Kaduna, Anthonia Sinbene ta bayyana cewa hukumar za ta horas da ma’aikatan wucin gadi 35,000 aiyukkan zaben da za a yi a watannin Faburairu da Maris.
Sinbene ta ce za a dauki kwanaki uku suna horas da wadannan mutane a kananan hukumomin dake jihar.
Ta kuma ce wadannan mutanen da za su horas za su shugabanci wasu fannonin aiyukkan zabe a rumfunar zabe 5,102 dake kananan hukumomin jihar.
Sinbene ta an samu matsalar cinkoson mutane a wuraren da suke samun horon domin wasu haka kawai suka bayyana a wurin ba tare da an Kira su ba.
Ta ce hukumar za ta horas da wadanda aka mutanen zabo daga cikin wadanda suka nemi aikin ne.
‘‘Mun aika wa wadanda muka zaba sakon tes a wayoyin su wanda hakan zai taimaka mana wajen tace duk wadanda ba su nemi aikin ba.
A karshe Sinbene ta ce hukumar ta a bukatar mutanen 3200 amma hukumar zata horas da mutanen 35,000 domin cike gurbin wadanda za su ki zuwa aikin idan aka Zabe su.
Discussion about this post