Ina da tabbacin samun nasara a wannan zabe – Inji Atiku

0

A yau Lahadi ne dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa bisa ga dukka alamu ba bayanan dake shigowa yana da tabbacin shine zai lashe zaben shugaban kasa.

Atiku ya ce ganin yadda ma’aikatan hukumar zabe ke aiki tukuru da na’urorin zamani domin samar da sakamakon da kowa zai amince da shi, nan da dan lokaci kadan ‘yan Najeriya za su fita daga kangin da wannan gwamnati ta saka su ciki.

Ya mika godiyar sa ga ‘yan Najeriya da suka fito suka kada wa jam’iyyar ruwan kuri’u.

Atiku ya kuma yi kira ga mutane da su kasa su, tsare sannan su raka kuri’un su saboda kada jam’iyya mai mulki ta juya abinda suka zaba.

Atiku ya yaba wa jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi a lokuttan zabe.

Share.

game da Author