Idan na yi nasara a zabe zan gyara matsalolin Na’urar tantance masu zabe – Inji Moghalu

0

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Young Peoples Party (YPP), Kingsley Moghalu ya koka kan yadda rashin aikin na’urar tattance katin masu zabe ya kawo matsala a yankunan su.

Moghalu ya fadi haka ne bayan ya kada kuri’ar sa da karfe 11:55 a jihar Anambra.

‘‘Na fito gida tun karfe takwas na safe domin kada kuri’a amma da na taras matsaloin da ake fama da shi da na’uran tattance katin zabe na koma gida sannan na sake dawowa wajen 12 na rana.

Moghalu yace da zaran ya ci zabe zai magance duk wadannan matsaloli da ake fama da su a lokacin zabe.

Bayan haka dan majalisar dokoki dake wakiltar Abakaliki/Izzi Sylvester Ogba shima ya koka da rashin aikin na’urar tattance katin zabe a rumfar zabe dake makarantanr firamare a Ndinkwegu Amagu karamar hukumar Abakaliki.

Ogba yace na’urar tattance katin zabe bai yi aiki ba har na tsawon awa daya kafin aka samu aka gyara.

Ya kuma jinjina yadda zabe ke tafiya cikin kwanciyar hankali cewa hakan na da nasaba ne da yadda aka wayar da kan mutane.

Tsohon sanata dake wakiltar shiyar Ebonyi ta Arewa Sylvanus Ngiji-Ngele ya jinjina yadda zabe ke gudana lafiya.

Dan majalisar dokoki na kasa mai wakiltan Ezza ta Kudu Lazarus Ogbe ya koka kan yadda wasu ‘yan tsagera suka kashe wani ejan dinsa da wani jami’in jam’iyyar PDP a Ndegu-Amagu mazaba ta daya rumfar zabe 002.

Ya ce duk da cewa yana juyayin mutuwar wadannan mutane amma yana sa ran cewa hakan da ya faru ba zai shafi sakamakon zaben da aka yi a rumfar ba.

Share.

game da Author