Shugaban Hukumar Hana Rashawa da Laifukan Zambar Kudade, EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana nasarorin da EFCC ta samu a fannin hura usur, wato kwarmata sirrin wadanda suka boye makudan kudaden sata.
Magu ya ce daga lokacin da aka shigo da tsarin zuwa watan Mayu na 2018, EFCC ta bankado naira biliyan 527 da kuma dala milyan 53 daga jama’a daban-daban.
Da ya ke magana a taron da kungiyar AFRILCIL ta shirya jiya Alhamis a Fatakwal, Magu ya ce shigo da tsarin kwarmato na hura usur na daya daga cikin hanyoyi muhimmai da ake bi ana karya lagon masu satar kudaden jama’a.
Magu, wanda jami’in EFCC na Shiyyar Fatakwal, Usman Muktar ya wakilta, ya kara da cewa ana samun gagarimar nasara sosai a tsarin fallasa India aka kimshe kudaden sata, ko a bankuna ko a gidaje ko ma a ina ne.
Sauran wadanda suka yi jawabai a wurin sun hada da Daraktan Kungiyar CORA mai fafutikar dakile rashawa, Chido Onumah da kuma wakilin Shugaban HUkumar CCB, Isokariari Sotonye.
Magu ya yi kira da a ci gaba da fallasa wadanda suka boye kudade domin.a gaggauta nasarar kawai da cin hanci da rashawa, wanda ya yi wa Najeriya katuti.