Hukumar Binciken Hatsarin Jiragen Sama ta Kasa (AIB), ta fara binciken sanadiyyar hatsarin helikwafta a garin Kabba, wanda ya ritsa da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, a ranar Asabar da ta gabata.
Janar Manaja na Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Kasa (NCAA), Sam Adurogboye ne ya bayyana haka jiya.
Sam ya ce tabbas hukumar AIB ta sanar da su cewa za ta fara bincike domin gano dalilin faduwar jirgin tare da mutane 12 da ke cikin sa.
Wata majiya da ba ta so a ambaci sunan ta, ta tabbatar da cewa tuni har wata tawagar jami’an AIB ta isa wurin da jirgin ya yi saukar gaggawa a garin Kabba, Jihar Kogi.
Cikin wadanda hatsarin ya ritsa da su, akwai Osinbajo, Ministan Kwadago da kuma Mashawarcin Shugaban Kasa a Harkokin Siyasa, Femi Ujudu.