Duk irin yadda masu nazari za su fassara zaben shugaban kasa da za a gudanar gobe Asabar, ko da ‘yan takarar sun kai yawan cikin carbi, to karshen ta dai cewa za a yi takara ce tsakanin mutum biyu, wato Shugaba Muhammadu Buhari na APC da kuma Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP.
Su biyu din nan duk kar-ta-san-kar ne, dukkan su babu kanwar lasa a cikin takarar. Ba kamar yadda Buhari ya yi nasara a zaben 2015 a kan Goodluck Jonathan ba, inda ya samu gagarimar goyon baya. Buhari a wannan lokaci ya na fuskantar matsaloli da dama.
Farin jinin jam’iyyar APC ya ragu,ba kamar 2015 ba lokacin da wasu jihohin ma ‘yan PDP tsoro su ke su nuna kan su, saboda goguwar Buhariyya ta mamaye ko’ina, musamman a Arewaci, tsakiyar Najeriya da kuma yankin Kudu maso Yamma.
Wani abin dubawa kuma shi ne, tun da APC ta kafa mulki, wadanda suka fice cikin jam’iyyar sun fi wadanda suka shige ta yawa. Yawancin gaggan da suke fice daga APC a fusace, masu jama’a ne, kuma da suka koma PDP, sun tafi tare da ilahirin mabiyan su. Sanata Rabi’u Kwankwaso, Aminu Tambuwal, Gwamna Samuel Ortom, Bukola Saraki duk babban misali ne a kan wannan. Ga kuma Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara.
Ita kuwa APC duk wadanda suka shige ta, yawancin su an fi yi musu yarfen siyasa cewa duk magen Lami ne, wadanda ba su dahakoran iya cizo, kuma ba su da kumbar susa. Sun shiga ne domin samun duhun da za su boye wa mafarautan da ke neman su daga EFCC.
Gagarimar nasar da APC ta samu a jihohin Jigawa, Kano, Benuwai, Filato, Kogi, Adamawa har ma da Sokoto, a wannan karo ba za ta same suba. A Kano ta tabbata cewa PDP za ta yi rinjaye ko kuma a yi kankankan.
Ko tantama babu APC za ta sha ruwan kuri’u a Jihohin Katsina, Barno, Yobe watakila har da Legas da wasu jihohin Yarabawa. Amma kuma PDP ita ma din za ta yagi kaso mai yawa a Legas da wasu jihohin yankin.
Jihar Ribas da PDP ta yagi kuri’u sama da miliyan biyu a 2015, a wannan zaben ma da alama za ta kwasa da dama.
Abin lura dai a nan shi ne, APC sai ta yi da gaske za ta iya kai labari. PDP kuwa idan ta yi dace ta samu kuri’un yankin Kudu maso Gabas, to shikenan, sai kawai a baku kofi a huta, wasa ya tashi.
Gobe dai ce ranar raba gardama. Idan aka kayar da Atiku, shikenan zai yi adabo da neman takarar shugabancin kasar nan. Idan kuma Buhari aka kayar, shi ma sai Daura kenan. Dama garken shanun sa na can, murnar cin zaben 2015 ba ta sa ya yi kauta da su ba.