Harin Boko Haram ba zai sare mana guiwa ba – Gwamna Shettima

0

Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima ya yi magana dangane da harin da Boko Haram suka kai wa tawagar sa ta yakin neman zaben a shekaranjiya Talata.

Shettima ya fito takarar sanata ne, kuma shi ne daraktann kamfen na dan takarar APC na gwamnan jihar Barno.

Gwamna ya yi magana ne a yau Alhamis, kwanaki biyu bayan kai masa harin a ranar Talata da yamma kwarai.

Yayin da ya koma Maiduguri a jiya Laraba da yamma, bayan rangadin yakin neman zaben, ya hadu da cincirinron ‘yn tarbar sa domin jajenta masa abin da ya faru.

A cikin wata takarda da kakakin yada labaran gwamna, Isa Gusau ya fitar a yau Alhamis, Shettima ya ce ya na jajaentawa tare da yin ta’aziyyar wadanda suka rasa rayukan su da kuma jaje ga wadanda suka ji raunuka.

Ya ce ba da daewa ba zai zagaya domin yin ta’aziyya da jaje ga iyalan wadanda harin ya taba.

Kashim ya ce zai kuma zauna da jami’an tsaro a yau din nan domin su ba shi cikakken bayanin lamarin da ya faru.

Gwamnan ya ce harin ba wani abu ba ne, tayar da kura ce kawai Boko Haram suka yi, domin su ja hankalin kafafen yada labarai na cikin gida da kuma na kasashen waje. Da kuma kokarin sun a nuna gazawar sojojin Najeriya.

Ya ce yi amanna kuma ya gamsu da irin namijin kokarin da sojojin Najeriya da jami’an sa-kai na CJTF ke yi domin murkushe Boko Haram dungurugum.

Ya roki jama’a da su kara kwantar da rayukan su kuma su ci gaba da addu’o’i, tare da fallasa duk wani bayanin da zai sa jami’an tsaro su yi nasara da galaba a kan Boko Haram.

Takardar ta ci gaba da bada labarin garuruwan da gwamnan ya je domin rangadin yakin neman zabe.

PREMIUM TIMES ta kawo maku cikakken labarin yadda Boko Haram su ka bude wa tawagar kamfen din Gwamna Kashim Shettima wuta.

Share.

game da Author