HARAJI: Gwamnatin ta fara farautar attajirai da basu biyan haraji 40,000

0

Shugaban Hukumar Tara Harajin Cikin Gida (FIRS), Tunde Fowler, ya bayyana cewa hukumar za ta fara farautar hamshakan attajiran da ke kin biyan haraji.

Da ya ke magana a lokacin da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu ya kai masa ziyara a Abuja, Fowler ya ce sun gama shiri tsaf wajen haka hannu da ‘yan sanda, domin tilasta wa attajiran biyan haraji.

Ya kara da cewa kwananan nan suka kammala tantance attajirai sama da 45,000, masu jarin sama da naira miliyan 100 a asusun ajiyar su na banki, inda aka tatsi harajin naira bilyan 23 a hannun su.

Ya ce akwai kuma wasu rukunin hamshakan allajiran har 40,000 da su ma ba su biyan haraji, wadanda za a hada hannu da ‘yan sanda, domin a tatsi haraji daga jarin kasuwancin su.

Fowler ya ce akwai kuma rukunin hamshakan attajirai wadanda jarin su ya kai naira milyan 999, wadanda su ma ana kan layin binciken asusun ajiyar su a bankuna daban-daban.

Wadanda ma ba su da lambar shaidar iznin harkokin kasuwanci ta TIN, inji Fowler, sun kai 45, 504, kuma ba su biyan kudaden haraji.

Gaba daya dai ya ce ya zuwa yanzu an samu attajirai 40,000 da ba su biyan haraji, wadanda ya ce cikin 2019 din nan za a fara farautar su.

Share.

game da Author