Gwamnan Benuwai ya ciwo wa PDP dukkan kuri’un rumfar sa

0

Jam’iyyar PDP ta lashe dukkan kuri’un da aka jefa a akwatinan mazabar da gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya jefa kuri’a.

Ortom yayi zabe ne a Mazabar Makarantar Sakandare ta Gbajimba, PU 003, da ke Mazabar Tsohuwar Kasuwa, a Nzoro, cikin Karamar Hukumar Guma.

Sakamako ya nuna cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya cinye kuri’un kakaf guda 711, yayin da Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC bai samu ko daya ba.

A yayin da ake gudanar da zaben, wakilin mu ya fahimci cewa akasarin mazabun da ke Gbajimba din babu ma ejan na jam’iyyar APC ko daya a wurin kowane akwatin zabe.

Ortom dai a karkashin APC ya ci zabe, amma daga baya ya koma PDP A CIKIN 2018.

Zai sake takarar gwamna nan da makonni biyu masu zuwa.

Share.

game da Author